Adadin Mutanen dake amfani da Facebook sun fi ýan ƙasar China yawa

Adadin Mutanen dake amfani da Facebook sun fi ýan ƙasar China yawa

- An bayyana yawan mutanen dake amfani da Facebook sun kai biliyan 2

- Mark Zunckeberg, mai kamfanin ne ya bayyana haka

Mamallakin shahararriyar kafar sadarwar zamanin nan ta Facebook, Mark Zuckerberg ya bayyana cewar adadin ma’abota shafin sun karu zuwa biliyan biyu a jiya Talata 27 ga watan Yuni.

Zuckerberg ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda yace “Da safiyar yau ne ma’abota amfani da Facebook suka kai mutane biliyan biyu”, haka zalika ya kara da cewa “A shekarar 2012 ne muka samu mutane biliyan guda dake amfani da Facebook.”

KU KARANTA: Atiku Abubakar ya jinjina ma muƙaddashin shugaban ƙasa Osinbajo

Yanzu kimanin shekaru 13 kenan da kafa shafin Facebook, tun bayan da Marka ya kammala karatunsa a jami’ar Harvard dake kasar Amurka.

Adadin Mutanen dake amfani da Facebook sun fi ýan ƙasar China yawa

Mai kamfanin Facebook

Mark Zuckerber ya bayyana burinsa shine ya hade al’ummar Duniya gabaki daya ta hanyar shafin Facebook, don haka yace:

Adadin Mutanen dake amfani da Facebook sun fi ýan ƙasar China yawa

Facebook

“Ba sai munyi ta wasa kan mu ba don mun samu mutane biliyan biyu, bukatar mu itace mu sadar da kowa da kowa.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani hukunci ya dace da Evans?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel