Babu wanda ya isa ya hana Buhari magana da Hausa – Inji Shehu Sani

Babu wanda ya isa ya hana Buhari magana da Hausa – Inji Shehu Sani

- Wani Sanata yace sakon da Buhari ya aiko ma yan Najeriya da Hausa yayi daidai

- Sanatan yace ai akwai mukaddashin shugaban kasa a Najeriya

Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewar babu wata matsala cikin sakon Barka da Sallah da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike ma yan Najeriya cikin yaren Hausa.

NAIJ.com ta ruwaito Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafin sadarwarsa na Facebook, inda yace tunda dai shugaban kasa baya kasa, kuma ya mika akalar mulki zuwa ga mataimakinsa a matsayin mukaddashin shugaban kasa, mukaddashin ne ya kamata yayi dinga yin magana da Turanci ba Buhari ba.

KU KARANTA: An kama shugaban ýan fashi da bindigu guda 5 a Abuja (Hotuna)

Sai dai Shehu Sani yace, tun a farko za’a iya kauce ma cece kucen daya dabaibaye hazo biyo bayan fitar da sakon daga shugaban kasa, amma “Mu cigaba da yi masa addu’ar samun sauki, tare da addu’ar zaman lafiya ga kasa

Babu wanda ya isa ya hana Buhari magana da Hausa – Inji Shehu Sani

Shehu Sani da Buhari

“Sa’annan ita ma fadar shugaban kasa ya dace ta dinga sanar da yan Najeriya halin da lafiyar shugaban kasa ke ciki domin kawar da shaci fadi da zantuttuka marasa tushe da madafa.” Inji Shehu Sani.

Cece kucen mako, kalla anan:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel