Ina goyon bayan gwamnatin gwamna Ganduje ɗari bisa ɗari – Sarkin Kano

Ina goyon bayan gwamnatin gwamna Ganduje ɗari bisa ɗari – Sarkin Kano

- Sarkin Kano Sunusi ya kai ma gwamna Ganduje ziyara a fadar gwamnati

- Sarkin ya kai ziyarar ne a hawan Nasarawa daya gudana a jiya

Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya bayyana cewa babu tantama a biyayyar da yake yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Daily Trust ta ruwaito Sarki Sunusi yana fadin haka ne yayin dayake gabatar da jawabi a ziyarar daya kai ma gwamnan jihar Kano a fadar gwamnatin jihar, inda yace:

KU KARANTA: Gwamna Wike ya tabbatar ma Musulman jihar Ribas tsaronsu da dukiyoyinsu

“Ina tabbatar ma gwamnatin tarayya data jihar Kano cikakiyar goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya a Najeriya, ya kamata mu zage damtse wajen wayar da kawunan matasan mu domin su fahimci muhimmancin zaman lafiya.”

Ina goyon bayan gwamnatin gwamna Ganduje ɗari bisa ɗari – Sarkin Kano

Sarki da Gwamna

Sarkin yayi kira ga gwamnatin jihar Kano data taimaka ma manoma kan wasu kwari da suke addaban gonaki a wasu kauyukan jihar, sa’annan ya shawarci musulmai dasu kyautata halayyarsu da darussan watan Ramadana.

Ina goyon bayan gwamnatin gwamna Ganduje ɗari bisa ɗari – Sarkin Kano

Jawabin Sarki

A nasa jawabin, majiyar NAIJ.com ta ruwaito gwamna Ganduje yana shawartar jama’ar Kano dasu zauna lafiya da juna, domin samar da cigaba mai daurewa a jihar.

Ina goyon bayan gwamnatin gwamna Ganduje ɗari bisa ɗari – Sarkin Kano

Ganduje da Sarki Sunusi

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli zantutukan Sarki Sunusi a Kano:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wata ‘Yar Majalisa tace barayi su ka daura Shugaba Buhari kan mulki

Wata ‘Yar Majalisa tace barayi su ka daura Shugaba Buhari kan mulki

‘Yar Majalisa ta zargi Shugaban Kasa Buhari da wani babban laifi
NAIJ.com
Mailfire view pixel