Baro-baro: Wani Minista ya tonawa 'Yan Majalisa asiri

Baro-baro: Wani Minista ya tonawa 'Yan Majalisa asiri

– Ministan ayyuka da wuta ya kara yin kaca-kaca da Majalisa

– Fashola ya zargi Majalisa da yin coge a kundin kasafin kudi

– Majalisar kuma ta maida masa martani wanda bai hakura ba

Takaddamar da aka tayi tsakanin Fashola da Majalisa ba ta kare ba. Fashola ya karyata ‘Yan Majalisar kasar baro-baro. Fashola ya koka inda yace wasu ‘Yan Majalisar ba su fahimci sha’anin kasafi ba.

Baro-baro: Wani Minista ya tonawa 'Yan Majalisa asiri

Minista Fashola ya tonawa Majalisa asiri

Ministan ayyuka da wuta Babatunde Raji Fashola ya kara yin kaca-kaca da Majalisar Kasar nan inda yace ba mamaki sun jahilci aikin kasafin kudi yake cewa ba su da ikon kirkiro sabon ayyuka cikin kundin kasafin kudin kasar.

KU KARANTA: PDP za ta karawa Ma'aikata albashi idan ta dawo mulki

Baro-baro: Wani Minista ya tonawa 'Yan Majalisa asiri

Wasu ‘Yan Majalisar Jahilai ne Inji Minista ayyuka

Majalisar tayi maza ta maida masa martani bayan ya zarge ta da coge inda tace yana nema ya zama Makaryaci. Fashola yace Majalisar ba ta maida martani kan abin da ya fada ba. Ministan dai yace Majalisa ta cire wasu manyan ayyuka ta saka na ta.

A makon jiya ne Hukumar zabe tace ta samu korafi daga Jama’ar Mazabar Yammacin Kogi na shirin maido Sanata Dino Melaye gida. Tuni dai aka sa rana domin tantance sa hannun Jama’ar domin daukar mataki na gaba.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dan tawaye yayi wa Jama'a jawabi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel