Wata sabuwar cuta mai lalata gonaki ta kuno kai a Jihar Filato

Wata sabuwar cuta mai lalata gonaki ta kuno kai a Jihar Filato

- Manoma a jihar Filato na fuskantar kalubale bayan da aka gano wata cuta dake barnata amfanin gona

- Jihar Filato na gaba gaba a wajen fannin noman kayan marmari

- Manoman sun kira hukumomin gwamnati da su kawo masu agajin gaggawa

Wata sabuwar cutar tsiro da manoma suka kasa tantance ta, ta na lalata gonaki masu yawan gaske a jihar Filato dake arewa maso tsakiyar nan.

Manoman su bayyana cewa lamarin ya janyo masu hasara da dama, ganin irin barna da wannan cutar ke yi wa itatuwa kamar na gwaiba, mangwaro da sauran itatuwa a karamar hukumar Qua'an pan da ke jihar.

Manoman da sun yi kira ga hukumomin gwamnati da su kawo masu dauki don kawo karshen wannan sabuwar cuta da ke ci gaba da addabar gonakin nasu.

Wata sabuwar cuta mai lalata gonaki ta kuno kai a Jihar Filato

Manoma a jihar Filato na fuskantar kalubale bayan da wata cuta mai lalata gonaki ta kuno kai a Jihar

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, shugaban sashen kula da lafiyar dabbobi a cibiyar binciken lafiyar dabbobi ta kasa dake Vom a jihar Filato, Farfesa Garba Hamidu Sharubutu, ya na cikin wadanda wannan sabuwar cutar ta addabi gonakinsu.

KU KARANTA: Kasa-daya-al'umma daya: Wani Inyamuri a Kano ya dinkawa Almajirai 30 kayan Sallah

Wani mai shari’a Thomas Naron da gonarsa ta kamu da wannan cutar, shi ma ya yi kira ga hukumomi da su kawo daukin gaggawa domin ceto gonakinsu.

Jihar Filato ce ta yi fice a fannin noman kayan marmari da ma hatsi

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel