Tunanin rashin aikin yi a Najeriya na hana ni samun bacci da daddare - Alhaji Aliko Dangote

Tunanin rashin aikin yi a Najeriya na hana ni samun bacci da daddare - Alhaji Aliko Dangote

Shugaban kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana babban abunda ke hanashi bacci da daddare.

Yace rashin aikin yi a Najeriya na hanashi samun bacci idan ya kwanta.

Dangote ya bayyana wannan ne yayinda ya gana da wasu manyan makarantan kasuwancin legas, yayinda suka kai ziyara sabuwar matatan man fetur din da ya gina a Ibeju-Lekki, Lagos.

“Ba wani harkan kasuwanci ke hana ni samun bacci da daddare face yadda rashin aikin yi ya yawaita a kasa.

“Wannan abu ta zama ciwon ido kuma wajibi ne mu hadu gaba daya mu shawo kan wannan abu."

Tunanin rashin aikin yi a Najeriya na hana ni samun bacci da daddare - Alhaji Aliko Dangote

Tunanin rashin aikin yi a Najeriya na hana ni samun bacci da daddare - Alhaji Aliko Dangote

“Yayinda talauci ke kara yawa a al’ummar da babu ilimi, yan baranda kawai za’a dinga kiwo."

“Abin mamaki ne cewa talauci na kara yawa yayinda mutane ke yawaita musamman a arewacin Najeriya inda iyaye maras hali ke haifan yaran da ba zasu iya kula da su ba.”

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Borno ta fara zagaye jami'ar Maiduguri

Dangote yace ba ba aikin gwamnatin bane samar da aiki. A kasashen da suka cigaba, ba gwamnati ke samarwa ba masu zaman kansu ne key i.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel