Za a shinge jami’ar Maiduguri don dakile hare- haren Boko Haram

Za a shinge jami’ar Maiduguri don dakile hare- haren Boko Haram

- An soma aikin zagaye jami’ar Maiduguri dagan dagan

- Wannan aikin nada nisan kilomita 27 kuma ta na bukatar naira miliyan 50

- Gwamnan Shettima ya ziyarci jami'ar Maiduguri bayan wata harin Boko Haram don gani wa idon sa barnan da ‘yan kuna bakin waken suka yi

An fara aikin zagaye jami'ar Maiduguri domin kare makarantar daga hare-haren ta’addancin kungiyar Boko Haram, a karkashin wani shirin gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ganin cewa an yi shingen jami’ar.

Sanarwar fara aikin wanda zai kai nisan kilomita 27 kuma zai ci naira miliyan 50, ta zo ne kwana guda bayan wasu 'yan kunar bakin wake sun kai hari a jami'ar, inda suka kashe kansu da kuma wata ma'aikaciya.

KU KARANTA: IBB ya caccaki masu neman wargaza Najeriya

Za a shinge jami’ar Maiduguri don dakile hare- haren Boko Haram

Hare-haren Boko Haram a jami'ar Maiduguri ya tilasta gina ramuka

A ranar Litinin, 26 ga watan Yuni ne gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya ziyarci jami'ar Maiduguri don duba ta'adin da maharan Boko Haram suka yi, yayin da kuma ya bayyana cewa tuni aka fara aikin gina shingen.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, gwamnan ya ce yanzu haka zagaye jami’ar ya zama dole ne domin dakile duk wani yunkuri 'yan ta'adda kai hari a kan jami'ar nan gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel