Jonathan ya kewaye kansa da miyagun mutane – Inji Unongo

Jonathan ya kewaye kansa da miyagun mutane – Inji Unongo

- Dattijo Dakta Paul Unongo ya ce miyagu ‘yan siyasa ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kewaye kansa da su

- Unongo ya ce Jonathan ya tsake wa kabilunsa har suka kwace masa gwamnati, inda suka ta wawushe dukiyoyin al’umman kasar

- Dattijon ya ce ya ziyarci Jonaathan don ya gaya masa karara cewa ba su sake zaben sa karo na biyu ba

Wani dattijo Dakta Paul Unongo, ya bayyana dalilan da yasa ya janye goyon baya ga tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan a zaben 2015 da ta gabata.

Dattijon ya ce Jonathan ya rasa ikon shugabanci kuma yana da rauni a shugaban kasar.

A cewar shi, tsohon shugaban ya tsake wa kabilunsa har suka kwace masa gwamnati, inda suka ta wawushe dukiyoyin al’ummam kasar.

Jonathan ya kewaye kansa da miyagun mutane – Inji Unongo

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Unongo ya saida wa jaridar NAIJ.com cewa Jonathan ba shida kwarewa gudanar da mulkin kasar kuma ya ki sauraron shawara daga dattijan kasar.

KU KARANTA: Fani-Kayode ya yi Allah wadai da kalaman shugaban ‘yan fafutukar Biyafara

A cewar shi: "Ina da dalili da yasa na ki zaben Jonathan karo na biyu. Na yanke shawarar cewa ba shida kwarewa gudanar da mulki a matsayin shugaban kasa. A yakin neman zaben shekarar 2011, na gaya masa a lokacin da ya je Makurdi cewa samu zabe shi, kuma mun cika alkawarin”.

"Kuma a lokacin da a ke shirin zaben shekara 2015, na ziyarce shi don na gaya masa cewa ba samu sake zaban sa karo na biyu ba”.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel