Kwankwaso ne ya dauki nauyin matasan arewa da suka bukaci ‘yan kabilar Igbo ficewa daga arewa – Inji shugabanin IPOB

Kwankwaso ne ya dauki nauyin matasan arewa da suka bukaci ‘yan kabilar Igbo ficewa daga arewa – Inji shugabanin IPOB

- Kungiyar 'yan asalin mutanen Biyafara na zargin tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabiu Musa Kwankwaso cewa yana goyon bayan matasan arewa

- IPOB ta ce wasu dattawan arewa ke tallafawa shugabanin kungiyoyin matasan arewan don musguna wa ‘yan kabilar Igbo da ke zaune a jihohin arewacin kasar

- Emma Powerful ya ce shugabanin kungiyar ba su tare da shugabanin yankin kudu maso gabashin kasar

Kungiyar 'yan asalin mutanen Biyafara wato IPOB, a ranar Litinin, 26 ga watan Yuli suka mayar da martani kan wani zance tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a kan ya kamata shugabannin kabilar Igbo su yi shika da masu fafutukar kafa Biyafara domin nuna gaskiya ga hadin kai kasar.

Abin lura a nan shine kalmomin tsohon gwamnan Kano da takun sa yana nuna goyon baya ne tallafawa ga shugabanin kungiyoyin matasan arewa da suka ba ‘yan kabilar Igbo wa’adin watanni uku ficewa daga jihohin arewacin kasar.

KU KARANTA: Jonathan shugaba ne mai rauni, ko uwargidarshi tafi shi izza – Nnamdi Kanu

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar sakataren harkokin watsa labarai ta kungiyar IPOB, Emma Powerful ya ce shugabannin kungiyar a duk duniya a karkashin jagorancin Nnamdi Kanu ba su tare da shugabannin kasar Igbo.

Sakataren ya ce: “Kwankwaso a yanzu haka ya bayyana mana manufarsa a cikin bayanin da yayi cewa yana daya daga cikin wasu dattawan arewa masu tallafawa matasan arewan don musguna wa ‘yan kabilar Igbo da ke zaune a jihohin arewacin kasar."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel