Jonathan shugaba ne mai rauni, ko uwargidarshi tafi shi izza – Nnamdi Kanu

Jonathan shugaba ne mai rauni, ko uwargidarshi tafi shi izza – Nnamdi Kanu

Mu’assasin Rediyo Biafra kuma shugaban kungiyar fafutkar neman yancin Biafra wato Indigenous People of Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu ya caccaki tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, kuma ya siffantashi a matsayin ummul khaba’isin matsalolin Najeriya.

Kanu ya siffanta Jonathan a matsayin shugaba mai rauni kuma gajiyayye wanda bai yiwa yankun kudu maso gabas komai ma duk da cewa yana ikirarin cewa shi dan yankin ne.

Kanu wanda yayi Magana da jaridar Sun a karshen makon da ya gabata yace uwargidarshi Patience ma zatafi mijinta kyau da shugabancin kasa.

Jonathan shugaba ne mai rauni, ko uwargidarshi tafi shi izza – Nnamdi Kanu

Jonathan shugaba ne mai rauni, ko uwargidarshi tafi shi izza – Nnamdi Kanu

Yace: “ Jonathan yayana ne. Ina daya gada cikin wadanda sukace gwamnatin Jonathan tamkar gwamnatin Igbo ne; lallai na fadi haka.

“Amma ya san bani shiri da gwamnatinshi saboda mai rauni ne kuma gajiyayye. Bana goyon bayan sharri,; idan ka kyautatata, zan fada ma, idan kuma kayi ba daidai ba, bana alfarma.”

KU KARANTA: Tsohon ministan noma ya samu karramawa a kasar waje

“ Mai rauni be, ni dana so ma Aunty Patience ce tayi shugabanci, da tafi aiki.”

“Kalli inda Jonthan ya ajiyemu a yau; bai gama ginin hanyar East/West Road ba, amma ya gina jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja, saboda su so shi.”

“Waya fada maka idan basu so ‘Zik’, zasu so ka?”

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel