Fani-Kayode ya yi Allah wadai da kalaman shugaban ‘yan fafutukar Biyafara

Fani-Kayode ya yi Allah wadai da kalaman shugaban ‘yan fafutukar Biyafara

- Fani-Kayode ya yi Allah wadai da kalaman shugaban 'Yan Asalin Mutane Biyafara, Nnamdi Kanu ya yi kan tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan

- Nnamdi Kanu ya ce Jonathan ba shida kwarewa ta yadda ake shugabancin kasa

- Fani-Kayode ya ce yayi imani cewa Jonathan shugaba ne mai kirki da jaruntaka

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya musanta zargin cewa tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ba shida kwarewa a lokacin da yayi shugabancin kasar.

Fani-Kayode ya maida martani ga kalaman da shugaban masu fafutukar kafa kasar Biyafara wato 'Yan Asalin Mutane Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu ya yi wa tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan cewa ba shida kwarewa ta yadda ake shugabanci.

Kanu ya ce kalaman Jonathan cewa ya kasance daya da ‘yan yankin kudu maso gabashin kasar yodara ne kawai. Ya ce babu abin da ya masu a yankin.

Fani-Kayode ya yi Allah wadai da kalaman shugaban ‘yan fafutukar Biyafara

Shugaban 'Yan Asalin Mutane Biyafara, Nnamdi Kanu

KU KARANTA: Dan tawaye Nnamdi Kanu ya yabi shuwagabannin arewa, ya soki Nnamdi Azzikiwe

Fani-Kayode ya rubuta a kan shafinsa ta Twitter cewa: "Ban yarda cewa Jonathan ya kasance mai rauni a mulkinsa ba. Na yi imani cewa Jonathan shugaba ne mai kirki da jaruntaka”.

NAIJ.com ta ruwaito cewa shugaban IPOB ya ci gaba da cewa shakka babu uwargidan tsohon shugaban kasar wato Patience Jonathan zata fi mijinta kwarewar a shugabanci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel