An kama shugaban ýan fashi da bindigu guda 5 a Abuja (Hotuna)

An kama shugaban ýan fashi da bindigu guda 5 a Abuja (Hotuna)

Jami’an rundunar yansandan babban birnin tarayya sun kama wani gawurtaccen dan fashi mai shekaru 25, Michael Olowu a kauyen Kabusa na babban birnin tarayya, Abuja.

Kwamishinan yansanda, Musa Kimo ya bayyana an kama Michael ne a ranar Laraba da misalin karfe 3 na yammacin ranar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Allah ya haska zuciyar wasu mata a watan Azumin Ramadana (Hotuna)

Kwamishinan yace barawon tare da abokan fashin nasa sun dira gidan wani ma’aikacin kotu ne, Olayinka Ayeni.

An kama shugaban ýan fashi da bindigu guda 5 a Abuja (Hotuna)

Dan fashin da sauran barayin wayan wuta

Tuni dai dan fashin ya amsa laifin ga yansanda, sa’annan na kwato makamai da suka hada da bindigu guda 5, alburusai, adda, wayan hannu, na’aurar kamfuta guda 2 da kudi naira 35,000, inji rahoton majiyar NAIJ.com.

A wani labarin kuma, rundunar ta kama mutane hudu da laifin satar wayar wuta, wadanda aka kama sun hada da Jonathan Duru, Chinedu Okafor, Uchenna Eke da Ifeanyi Nnaji.

Kwamishinan yace an kama barayin ne a lokacin da suka yanke wayar wuta a Games Village, suma a tare dasu an kama diga guda 2, shebur guda 2.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Cecekucen mako:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel