Hukumar kwastam ta tattara ma gwamnati naira biliyan 239 a watanni 4

Hukumar kwastam ta tattara ma gwamnati naira biliyan 239 a watanni 4

- Kididdiga ta nuna hukumar kwastam ta tara makudan biliyoyi a wata 4

- Hukumar ta samu wannan nasara ne a karkashin jagorancin Hamid Ali

Hukumar yaki da fasa kauri ta kasa ta samar ma gwamnati da kudaden shiga da suka kai naira miliyan 239 a watannin ukun farko na bana, kamar yadda ma’aikatar kudi ta bayyana.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito cewar kudaden da hukumar ta kwastam ta tara sun kere adadin kudaden da ta kudirta Tarawa a watannin hudun farko a na shekarar.

KU KARANTA: Likafa ta cigaba: Tsohon ministan noma ya samu kyautan naira miliyan 90

Sanarwar ta kara da cewa, an samu wannan nasara ne biyo bayan garanbawul da aka gudanar a hukmar da kuma horar da jami’an ta, tare da sawwaka tsare tsare ayyukan hukumar.

Hukumar kwastam ta tattara ma gwamnati naira biliyan 239 a watanni 4

Hamid Ali

“Kwatsam ta tara naira biliyan 904.07 a shekarar 2015, wanda yayi kasa da abinda take nema, Naira biliyan 944.4, haka ma a shekrar 2016 an samu nukusani, inda ta tara biliyan 898.67, maimakon biliyan 973.3. Amma sai gashi daga watan Janairu zuwa Maris an 2017, hukumar ta tara biliyan 239.4” inji sanarwar

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito, hukumar ta bi umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya bukaci da’a aika da duk kayayyakin da hukumar ta kwace zuwa sansanonin yan gudun hijira a Yobe, Borno, Adamawa da Bini.

Daga karshe, Sanarwar tace a yanzu haka hkumar ta hau hanyar dodar don inganta ayyukan ta tare da tabbatar da gakiya a al’amuranta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Najeriya, giwarAfirka, da gaske?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel