Muryar Buhari ta ba yan Najeriya da dama tsoro - Rahoto

Muryar Buhari ta ba yan Najeriya da dama tsoro - Rahoto

- Wasu masu sharhi a Najeriya suna fargabar cewa rashin lafiyar Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ta tabarbare bayan da ya aike da sakon saukin muryarsa.

- Shugaban ya aike da saƙon bikin ƙaramar sallah ne ga 'yan Najeriya ranar Asabar.

- Lokacin ne karon farko da aka ji duriyarsa bayan ya kwashe kwana 49 yana jinya a Birtaniya.

NAIJ.com ta samu labarin cewa hakan ya sa jama'a sun rika bayyana ra'ayoyinsu a kafofin sada zumunta a kasar, inda wasu suke cewa "muryarsa tana nuna cewa rashin lafiyarsa ya yi tsanani."

Yayin da wasu ke cewa muryarsa ba ta sauya ba daga yadda suka santa ranar da zai tafi jinya Landan.

Malam Kabiru Danladi Lawanti na Fannin Koyar da Aikin Jarida na Jami'ar Ahamdu Bello ta Zariya, ya ce halin rashin lafiyar "shugaban ya yi tsanani."

Muryar Buhari ta ba yan Najeriya da dama tsoro - Rahoto

Muryar Buhari ta ba yan Najeriya da dama tsoro - Rahoto

"Duk wanda ya san Shugaba Buhari kuma ya saurari muryar da aka sanya ranar Asabar to wajibi ne ya tsorata."

"Za ka ji muryar tana shakewa kamar wanda ya kamu da mura." in ji Lawanti.

Ya ci gaba da cewa: "Idan ka saurari muryar da kyau za ka ji babu kuzarin da aka saba ji idan yana magana."

Har ila yau, malamin jami'ar ya yi tsokaci game da kiraye-kirayen da wasu ke yi na cewa lokaci ya yi da shugaban zai yi murabus.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel