Jam'iyyun PDP da APC duka abu guda ne – Inji Nuhu Ribadu

Jam'iyyun PDP da APC duka abu guda ne – Inji Nuhu Ribadu

- Tsohon dan takarar shugabancin kasa a Najeriya, Malam Nuhu Ribadu, ya ce babu wani bambanci tsakanin jam'iyyar APC mai mulki da kuma jam'iyyar adawa ta PDP a kasar.

- Sai dai tsohon shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin ta'annati (EFCC) ya ce da gaske gwamnatin Muhammadu Buhari take yi wurin yaki da cin hanci da rashawa.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Malam Nuhu shaida wa BBC cewa kudaden da ake kwatowa da wurin barayi da kuma gurfanar da su da ake yi a gaban kuliya sun nuna cewa gwamnatin Buhari ta kama hanyar kawo karshen cin hanci da rashawa a Najeriya.

A cewarsa, "Gwamnati na kokari matuka. Da ma niyya ake so mai kwari; idan aka samu shugaba na gari wanda ya ce ba ya son cin hanci, to za a samu mafita.

Sannan an karbe dukiyoyin da aka sace. Idan ka je babban bankin Najeriya za ka ga kudin da aka kwato. Wannan aiki ne na bangaren zartarwa".

Tsohon dan takarar shugaban na Najeriya ya roki sauran bangarorin gwamnati - alkalai da majalisa - sun zage dantse wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Jam'iyyun PDP da APC duka abu guda ne – Inji Nuhu Ribadu

Jam'iyyun PDP da APC duka abu guda ne – Inji Nuhu Ribadu

Ya ce lokacin da yake jagorancin EFCC, an kama mutane da yawa kuma an hukunta su, yana mai yin watsi da zargin da ake yi masa na cewa ya zama karen farautar tsogon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo inda ya rika tuhumar masu adawa da waccan gwamnatin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel