Wani Gwamnan Kudu ya dukufa da addu’o’i domin Shugaba Buhari

Wani Gwamnan Kudu ya dukufa da addu’o’i domin Shugaba Buhari

– Gwamnan Jihar Kuros Riba yayi wa Shugaba Buhari a addu’a

– Haka kuma Gwamnan Jihar Kaduna ya nemi a sa Shugaban a addu’a

– Sai kwanan nan aka ji muryar Shugaban Najeriyar tun barin sa kasar

Gwamna Ben Ayade yace yana nan yana ta yi wa Shugaba Buhari addu’a. Farfesa Ayade yace da shi da Jama’ar sa kullum sai sun yi wa Buhari addu’a. Kwanan ne Shugaba Buhari ya aiko sakon Sallah ga ‘Yan Najeriya da Hausa.

Wani Gwamnan Kudu ya dukufa da addu’o’i domin Shugaba Buhari

Gwamna Ayade ya saka Shugaba Buhari a addu’a

KU KARANTA: Ya kamata Buhari ya ajiye mulki Inji wani tsohon Janar

Wani Gwamnan Kudu ya dukufa da addu’o’i domin Shugaba Buhari

Shugaba Buhari tare da Ayade a Villa

Mai girma Gwamnan Jihar Kuros Riba Ben Ayade yace shi da mutanen Jihar sa sun dage ba dare ba rana wajen yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a ya samu lafiya. Gwamnan ya bayyana haka ne a sakon sa na goron Sallah.

Gwamna Ayade ya nemi Ubangiji ya ba Shugaban kasar karfi ya dawo ya cigaba da jagorancin kasar. Haka shi ma Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya nemi a sa kasa da Shugaban kasa addu’a a halin da ake ciki.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko Evans zai zama Shugaban kasa nan gaba [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel