Likafa ta cigaba: Tsohon ministan noma ya samu kyautan naira miliyan 90

Likafa ta cigaba: Tsohon ministan noma ya samu kyautan naira miliyan 90

- Cibiyar abinci ta duniya ta karrama Akinwumi Adesina

- Adesina ya kasance minista a gwamnatin tsohon shugaban kasa Jonathan

An bayyana tsohon ministan harkokin noma a Najeriya, kuma shugaban bankin ciyar da bankin samar da cigaba a Afirka, Akinwumu Adesina a matsayin gwarzon samar da abinci na shekarar 2017.

Karramawa na zuwa ne tare da kyautan kudi dala 250,000, kimanin naira miliyan casa’in kenan domin bayarwa ga duk wanda ya taimaka wajen ciyar da al’umma gaba ta hanyar samar da ingantattun kuma isassun abinci a Duniya.

KU KARANTA: Tabdijam! Wani Sarki ya hada akidar addinin Musulunci, Kirista da na gargajiya duka (Hotuna)

Shugaban cibiyar abinci ta duniya, Kenneth Quinn ne ya sanar da sunan Adesina a ranar Litinin, 26 ga watan Yuni yayin wani taro a ma’aikatar noma na kasar Amurka wanda ya samu halartan ministan harkokin nona na kasar Amurka, Sonny Perdue.

Likafa ta cigaba: Tsohon ministan noma ya samu kyautan naira miliyan 90

Tsohon Minista Adesina

Quinn yace “Mutanen da muke karramawa sun bada gudunmuwa sosai wajen magance matsalar yunwa a shekatu 30 da suka gabata.”, “Mun lura da kokarin da Adesina yayi wajen samar da takin zamani ga manoma tare da samar da kudade ga manoma. Da kuma kokarinsa na dakile cin hanci da rashawa a sha’anin samar da taki a Najeriya.”

Dayake nasa jawabi, Adesina ya bayyana ma jaridar All Africa cewar yayi matukar samu farin cikin da wannan karramawa, amma wannan karin kwarin gwiwa ne kawai domin yayi kara zage damtse.

NAIJ.com ta kawo muku bidiyo kan ko zaka iya auren tsohuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel