An cafke gangan ‘yan fashi da garkuwa da mutane da suka addabi jihar Katsina

An cafke gangan ‘yan fashi da garkuwa da mutane da suka addabi jihar Katsina

Rundunar ‘Yan sanda jihar Katsina ta bayyana wa manema labarai nasarar cafke wasu rukakkun ‘yan fashi tare da yin garkuwa da mutane har su hudu a karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina .

A lokacin da yake yi wa manema labarai karin haske game da nasarar cafke barayin, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina Abdullahi A. Usman ya bayyana cewa yan sandan jihar sun yi nasarar cafke yan fashin a ranar 18 ga watan Yuni da misalin karfe 3:30am na dare.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Kwamishinan ya ce wadanda ake zargin sun hada da; Halliru Auwal daga Kaduna,da Hassan Bello daga Kafur, da Dahiru Haruna daga Kusada da kuma Haruna Musa daga Kaduna.

An cafke gangan ‘yan fashi da garkuwa da mutane da suka addabi jihar Katsina

An cafke gangan ‘yan fashi da garkuwa da mutane da suka addabi jihar Katsina

Yace wadanda aka cafke duka duka ba su wuce shekaru 30 da haihuwa ba .

Katsina Post ta binciko cewa barayin an cafke su tare da wata karamar matarsu kirar Golf tare da tsabar nairori har N140,000, 19, da kuma tarin wayoyin hannu iriiri a hannun su.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel