Hare haren ƙunar baƙin wake yayi ƙamari a jami’ar Maiduguri, rayuka 16 sun salwanta

Hare haren ƙunar baƙin wake yayi ƙamari a jami’ar Maiduguri, rayuka 16 sun salwanta

Biyo bayan hare haren kunar bakin wake da aka kai a cikin jami’ar Maiduguri a ranakun Lahadi da Litinin, hukumar yansandan jihar ta bayyana cewar jimmillan mutane 16 ne suka rasu, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Kwamishinan yansandan jihar Borno, Damian Chukwu ne ya shaida haka, inda yace “Mun samu gawa 16, tare da mutane 13 da suka jikkata.”

KU KARANTA: Riba biyu: Ta maido da N19,000 kuɗin tsintuwa, an bata tukuicin N200,000

A daren Litinin da misalin karfe 10 na dare, an samu wata yar kunar bakin wake da ita ma ta tayar da kanta gab da shingen sojoji na jami’ar Maiduguri, inji kwamishinan.

Hare haren ƙunar baƙin wake yayi ƙamari a jami’ar Maiduguri, rayuka 16 sun salwanta

Jami’ar Maiduguri

Haka zalika majiyar NAIJ.com ta ruwaito kwamishinan yana fadin, an jiyo karar tashin bom a kananan hukumomin Zanari da Jere, yayin da wasu yan kunar bakin wake su biyu suka kai kashe mutane 8, tare da jikkata 11.

Hare haren ƙunar baƙin wake yayi ƙamari a jami’ar Maiduguri, rayuka 16 sun salwanta

Hain ƙunar baƙin wake jami’ar Maiduguri

Daga karshe ya kara da cewa wata yar kunar bakin wake ta mutu bayan an kamata, sakamakon raunukan data samu daga tashin bamabaman abokan aikinta, bugu da kari yan mata biyu sun sake kai hari a ranar Litinin da misalin karfe 8 na dare a jami’ar ta Maiduguri.

Hare haren ƙunar baƙin wake yayi ƙamari a jami’ar Maiduguri, rayuka 16 sun salwanta

Harin ƙunar baƙin wake a jami’ar Maiduguri

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yakin Sojoji da Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel