Tamkar yaƙin Kandak, za’a haƙa ramuka don daƙile harin Boko Haram a Maiduguri (Hotuna)

Tamkar yaƙin Kandak, za’a haƙa ramuka don daƙile harin Boko Haram a Maiduguri (Hotuna)

- Gwamna Kashim shettima zai gina ramuka da za'a zagaye jami'ar Maiduguri

- Za'a gina ramukan ne sakamakon harin kunar bakin wake

Gwamnatin jihar Borno ta amince da kashe naira miliyan 50 don cigaba da haka ramuka da zasu zagaye jami’ar Maiduguri domin dakatar da yawan samun harin kunar bakin wake a jami’ar.

Gwamna Kashim Shettima ne ya bayyana haka yayin ziyarar gani da ido daya kai a wajen aikin, inda yace sun dauki wannan mataki ne sakamakon ta wannan hanya ne yan kunar bakin waken ke samun damar shiga jami’ar.

KU KARANTA: Kungiyar ýan ta’adda ta tashi Masallaci mai shekaru 800 ta hanya harba bamabamai (HOTUNA)

A satukan da suka gabata, majiyar NAIJ.com ta bayyana cewar Kashim ya amince da kashe makudna kudaden ne saboda biyan kudin aikin ramukan, da na biya masu gadi na musamman da za’a kawo jami’ar.

Tamkar yaƙin Kandak, za’a haƙa ramuka don daƙile harin Boko Haram a Maiduguri (Hotuna)

Ramukan

Gwamnan yace ramukan zasu taimaka ma Sojoji wajen hangen yan kunar bakin waken tare da samun damar barar dasu daga nesa, kamar yadda Sahara Reporters suka ruwaito.

Tamkar yaƙin Kandak, za’a haƙa ramuka don daƙile harin Boko Haram a Maiduguri (Hotuna)

Gwamna

Mai rikon mukamin shugaban jami’ar, Farfesa Aliyu Shugaba, yayin dayake zagayawa tare da gwamnan ya bayyana godiyarsa ga yunkurin gwamnatin jihar, sa’annan yace sun mika kokon bara ga gwamnatin tarayya na gina Katanga domin zagaye sauran bangaren jami’an.

Tamkar yaƙin Kandak, za’a haƙa ramuka don daƙile harin Boko Haram a Maiduguri (Hotuna)

Aikin ramuka

Harin kunar bakin wake na ranar Lahadi shine na biyar da aka kai ma jami’ar a yan kwanakin nan, inda mahara su bakwai suka afka cikin jami’ar, dukkaninsu mata, sa’annan suka tashi kawunansu da bom. A yanzu haka dai dalibai suna hutu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Me ya kamata ayi ma mai garkuwa da mutane?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel