'Duk Wanda ya zaci Najeriya zata zauna kasa daya, lallai gaula ne' - Inji Olu Falae

'Duk Wanda ya zaci Najeriya zata zauna kasa daya, lallai gaula ne' - Inji Olu Falae

- Olu Falaye dai tsohon dan takarar shugaban kasa ne a jam'iyyar SDP

- Ya rike mukamin Sakataren gwamnati a zamanin mulkin soja

- Ya yi hira da Hakim Badamasi na jaridar Tribune

A hirarsa da wakilin jaridar Tribune, Hakim Badamasi, dattijon kasa daga kabilar Yarabawa, Olu Falae yayi tsokaci kan batun rarrabuwar kan kasa, rashin lafiyar shugaba Buhari, da ma makomar siyasar Najeriya.

Da aka tambaye shi kan batun zafafan kalamai da ke fitowa daba bakin manyan kabilun kasar nan, sai yace, ai dole a koma kan rahoton taron kasa da aka yi a shekarar 2014, a karkashin mulkin shugaba Jonathan, wanda ya yi kira da a koma a sake tsara Najeriya kan shiyyoyi.

'Duk Wanda ya zaci Najeriya zata zauna kasa daya, lallai gaula ne' - Inji Olu Falae

'Duk Wanda ya zaci Najeriya zata zauna kasa daya, lallai gaula ne' - Inji Olu Falae

"An yi taro na manyan dattijan kasar nan, an kashe kudi da lokaci, an fitar da ra'ayoyin jama'un kasa, kan nuna yadda suke so kasar nan ta zama, amma wannan gwamnatin ta yi biris da rahoton, dole a koma kan wannan in dai ana so kasar ta zauna lafiya cikin hadin kai'," Olu Falaye ya ce.

An kuma tambayi dattijon kan batun ko wai a zaben 2019, jam'iyyun PDP da tashi ta SDP mai magoya baya a kudancin kasar nan, sai ya ce, "a'a, ba wannan batun, amma muna maraba da duk wani mai son hadin kai da mu, kuma mai son bin tsarin jam'iyyar mu. Kai ko tsohon abokina ne shugaba Buhari ke son hadin kan APC da SDP muna maraba dashi."

Olu Falae dai ya zargi gwamnoni da hadiye jam'iyyun su kuma da bin abin da suka ga dama ba wai lalle ra'ayin jarm'iyya ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel