Junaid Muhammed ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari kan yin magana da Hausa

Junaid Muhammed ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari kan yin magana da Hausa

- Junaidu Muhammed tsohon dan majalisar wakilai ne

- Samarin kungiyar kungiyar Ijaw masu arzikin man fetur sun yi kumfar baki

- Buhari ya bada sakon sallah da Hausa bayyi fassara da turanci ba

Ana ta ci gaba da mayar da martani kan batun sakon sallah da shugaba Buhari yayi da yaren hausa, inda wasu ke kare shugaban, wasu ko ke zarginsa da bangaranci da kabilanci ganin cewa wasu da yawa daga masoyansa bassu jin yaren na Hausa.

Junaid Muhammed ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari kan yin magana da Hausa

Junaid Muhammed ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari kan yin magana da Hausa

A wannan karon Junaidu Muhammed ne, yayi tsokaci, inda yace sakin muryar ta shugaban a wannan lokacin, farfaganda ce kawai. A nasa ganin ma, shugaban bai kyauta wa 'yan Najeriya da ke jiran jin muryarsa ba, amma suka ji shi da yare na bangare ba na tsakiya ba.

"Ni banga dalilin sakin ma faifan muryar ba, in ba neman magana ba, kuma hadimansa ne da wannan aika-aikar, mu dai fatan mu samun saukin shugaban da kuma dawowarsa lafiya."

A nasu bangaren suma kabilar Ijaw, ta hannun mai yada sadarwar su, Henry Iyalla, shima ya ce magana da yaren Hausan bayyi musu dadi ba, ganin bangaren arewa ne kawai ke jin yaren.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel