'Yan Sandan Farin Kaya (DSS) sun kama shugaban 'yan Boko Haram da wasu da ake zargi guda 30 a Jihar Kano

'Yan Sandan Farin Kaya (DSS) sun kama shugaban 'yan Boko Haram da wasu da ake zargi guda 30 a Jihar Kano

- Sun so kai hari a Kano lokacin bukukuwan Sallah

- An kama guda 30 da shugaban su

- Ya tona maboyar sauran mayakan

Duk da gwamnati tace taci galaba a kan yaki da Boko Haram, har yanzu dai suna iya kai hari a garuruwa musamman a lokuta irin na bikin Sallah.

Hukumar 'yan Sandan boye na Jahar Kano a ranar Lahadi sun ce sun kama manyan 'yan boko haram guda 30 tare da kayan ta'addanci.

'Yan Sandan Farin Kaya (DSS) sun kama shugaban 'yan Boko Haram da wasu da ake zargi guda 30 a Jihar Kano

'Yan Sandan Farin Kaya (DSS) sun kama shugaban 'yan Boko Haram da wasu da ake zargi guda 30 a Jihar Kano

A yayin da shi Daraktan Alhassan Muhammad na ofishin Kano ya bada rahoton cewa binciken ya hada da 'yan sanda ne da kuma hukumar 'yan sandan farin kaya. si ya haifar da kama babban shugabansu da kuma wasu da ake zargi guda 30 yayin da suke shirin kai hari a bikin sallah a birnin Kano da wasu manyan jihohin arewa.

Yayi bayani cewa binciken ya dau tsawon awa 48 shi ya bada nasarar yin bikin sallah lafiya a jihar, in ba don hakan ba da an sami mummunan labari mara dadin gaske.

A kalamanshi ya ce: "a yanzu haka a hannunmu muna rike da wanda ake zargi 'yan Boko Haram ne guda 30 da kuma shugaban su na wanni bangaren da aka kama a unguwar Rijiyar Zaki da Dorayi a cikin kwanaki biyu."

Muhammad ya sani cewa wannan kokarin da sukayi shi ya samar da rashin faruwar hakan a Jihar Kano da wasu Jihohin a yayin bikin sallah.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne hukumar ta bayyana cewa ta kama wasu 'yan ta'adda da suke shirin kia hari a Jihar Kano, Kaduna, Sokoto da Maiduguri.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel