Ku zabi sabon shugaba idan baku gamsu da mulkin Buhari ba - Inji Sarkin Ife

Ku zabi sabon shugaba idan baku gamsu da mulkin Buhari ba - Inji Sarkin Ife

- Kuyi amfani da kuri'ar ku wajen canza shugabancin da baku gamsu da shi ba - Sarkin Ife

- Yan Najeriya basu san karfin da doka ta basu ba -Inji Sarkin Ife

- Sarkin Ife ya shawarci yan Najeriya da su daina zage-zage a tsakaninsu.

Sarkin Ife, Adeyeye Ogunwusi ya shawarci 'yan Najeriya da su zabi sabon shugaba idan basu gamsu da salon mulkin wannan gwamnatin ba.

Yayi wannan jawabin ne a wata hirar da aka yada a shirin Osasu.

Basaraken ya cigaba da cewa masu zabe ya kamata su san mahimmancin da suke dashi kuma yayi kira da su hada kansu waje daya domin cin ma matsaya kwakwara da zai amfane su baki daya.

Ku zabi sabon shugaba idan baku gamsu da mulkin Buhari ba -inji Sarkin Ife

Ku zabi sabon shugaba idan baku gamsu da mulkin Buhari ba -inji Sarkin Ife

Da aka tambayi shi abin da yake bukata gwamnati tayi domin kyautata rayuwan jama'a, Ba saraken ya amsa da cewa "Mene yasa dole sai mun jira gwamnati? Wacece gwamnatin? Ai mutane ne ku gudanar da gwamnatin.

"Idan baku gamsu da salon mulkin shugaban kasar ku ba, idan babban zaben shekara ta 2019 yazo, kuje kuyi amfani da kuri'ar ku domin ku tumbuke shi, idan kuma kun gamsu da salon mulkin nasa, sai ku zabe shi domin ya cigaba da mulki.

"Maganan gaskiya shine mutanen Najeriya musamman matasa basu san irin karfi da iko da suke dashi ba, musamman wajen zabe. Idan da mutane zasu gane wannan girman da suke da shi, zasu daina kuka da gwamnati.

"Ni akida ta shine, mutane su hada kansu waje daya domin su tattauna matsalolin da ke addaban kuma a samu mafita. Ya kamata mu daina zage-zage da fadin kalmomin battanci ga junanmu domin irin wadannan abubuwan zasu kara raba kan mutanen Najeriya ne."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel