Sakon Sallah: 'Buhari ya mayar da mu kasar wawaye' - Ohanaeze

Sakon Sallah: 'Buhari ya mayar da mu kasar wawaye' - Ohanaeze

- Buhari ya turo sakon sallah da Hausa

- Sauran mutan Najeriya sun so yayi da turanci

- Shugaba Osinbajo yace shugaban zai gama mulkinsa

A bukukuwan karamar sallah da ake yi a Najeriya, shugaba Buhari ya aiko da sako da yaren Hausa na murnar sallah ga musulmai 'yan Najeriya, wadanda galibinsu Hausawa ne da basa ma jin turanci.

Sai dai hakan bai yi wa wasu kabilun kasar nan dadi ba, ganin cewa makonni da yawa ba'a ji duriyarsa ba, tun bayan tafiyarsa kasar Ingila jinya. A ganinsu, duk wani sako, ya kamata shugaban yayi da yaren turanci.

Sakon Sallah: 'Buhari ya mayar da mu kasar wawaye' - Ohanaeze

Sakon Sallah: 'Buhari ya mayar da mu kasar wawaye' - Ohanaeze

A cewar shugaban kabilar Ibo, Ohanaeze Ndigbo, ta hannu mataimakinsa na harkar yada labarai Chuks Ibegbu, yace da farko ma dai babu tabbas shugaba Buharin ne yayi wannan kalami, in kuma shi yayi, to lalle da sake, don wannan raini ne ga kabilun Najeriya.

"Idan aka tabbatar shugaba Buhari ne yayi wannan Magana ta sakon sallah da hausa, to lallai ya mayar da mutan kasar nan ‘yan Banana Republic, (wata kasa da ake dabbakawa a matsayin kasar kama-karya)," ya fadi.

"Ai ma ba lallai shugaban ne yayi maganar ba, domin kuwa a zamanin nan na kere-kere da hade-hade, kowa zai iya hada murya yace ta shugaban ce, wanda ake zargin ma rashin lafiya ta hana shi magana." Ibebgu ya kara da cewa.

Ana dai ta cece-kuce kan ko da gaske shugaban ne yayi Magana ko kuma a’a, kuma ana zarginsa da bangaranci domin baiwa yarensa na ‘yan arewa fifiko.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel