Sakon murya na Sallah da Buhari ya aiko a harshen Hausa ya haifar da suka mai tsanani

Sakon murya na Sallah da Buhari ya aiko a harshen Hausa ya haifar da suka mai tsanani

- Sakon shugaban kasa Buhari na ci gaba da haifar da cece-kuce a tsakanin ‘yan Najeriya

- Fadar shugaban kasa ta saki sakon murya na Buhari don yin watsi da rahotanni dake cea yana fama da matsalar rashin magana

- ‘Yan Najeriya basu ji dadin yadda shugaban kasar ya aika sakon a harshen Hausa

Sakon barka da Sallah da shugaba Muhammadu Buhari ya aikawa ‘Yan Najeriya da harshen Hausa ya janyo cece-kuce da muhawara a kasar inda wasu ke ganin da harshen kasa na Ingilishi ya kamata shugaban ya yi amfani da shi.

Sai dai harshen Hausa da shugaban ya yi amfani da shi a sakon ya janyo cece-kuce da muhawara a Najeriya, inda wasu ke ganin Ingilishi ne harshen kasa da shugaban ya kamata ya aikawa ‘yan Najeriya da sakon.

KU KARANTA: Fani-Kayode ya soki shugaba Buhari kan sakon murya na sallahFani-Kayode ya soki shugaba Buhari kan sakon murya na sallah

NAIJ.com ta tattaro martani wasu 'yan Najeriya.

Sakon na tsawon minti daya da Sha’aban Ibrahim Sharada mai taimakawa Buhari wajen watsa labarai ya aikawa manema labarai a jajibirin Sallah shi ne na farko tun lokacin da shugaban ya koma London domin diba lafiyarsa.

Wasu rahotanni sun ce gwamnati ta fitar da sakon muryar ne domin yin watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa rashin lafiyar da ke damun shugaban har ta kai ba ya iya magana.

A halin da ake ciki NAIJ.com ta rahoto cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode ya yi zargin cewa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari bane ya yi magana a sakon murya da aka saki a jiya sallah.

Fani Kayode wani jigon jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a shafin tweeter ya ce: “Ba shugaban kasa Buhari bane ya yi magana a sakon murya na sallah da aka saki. Sannan kuma koma wanenene yay i jawabi ga kasar cikin harshen Hausa bai kyauta ba.”

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel