Yan Najeriya na son su sani shin shugaba Buhari zai iya cigaba da mulki, ba wai iya magana ba - Osuntokun

Yan Najeriya na son su sani shin shugaba Buhari zai iya cigaba da mulki, ba wai iya magana ba - Osuntokun

- Yan Najeriya na son su sani idan Shugaba Buhari zai iya cigaba da mulki -Osuntokun

- Yin magana baya nuna cikakiyar lafiyar Shugaba Buhari - Osuntokun

- Wasu sun maida mulkin Najeriya abin wasa - Osuntokun

Tsohon mai bada shawara ga shugaba Obasanjo akan harkokin siyasa, Akin Osuntokun ya sharhi akan rade-radin matsalar iya magana da ake zargin shugaba Buhari yana fama da ita. Ya misalta zargin da "bata lokaci akan lamarin da baida mahimmanci"

Wannan korafin dai ya taso ne bayan Shugaba Buhari ya aike da sakon murya domin taya mutane Najeriya murnar bukin Sallah karama.

KU KARANTA KUMA: Sakon Shugaba Buhari na bikin Idi ya kawo matsala

Yan Najeriya na son su sani shin shugaba Buhari zai iya cigaba da mulki, ba wai iya magana ba - Osuntokun

Yan Najeriya na son su sani shin shugaba Buhari zai iya cigaba da mulki, ba wai iya magana ba - Osuntokun

Ya cigaba da cewa kokarin nuna cewa Buhari bai da matsalar magana ba shi bane abin da yan Najeriya ke son su sani, mutanen Najeriya suna son su sani ne idan shugaba Buharin yana da cikaken lafiya da zai iya cigaba da gudanar da ayyukan ka a matsayin shugaban kasa.

"Rashin iya magana kawai ba shi ne rashin lafiyar da ka iya hana mutum zauka daga madafin mulki ba" Inji Osuntokun.

A wata hira da yayi da yan jarida a birnin Legas, ya shaida musu cewa iya magana shugaba Buhari ko rashin iya maganan ba shine abin da yafi mahimmaci ga mutanen Najeriya ba.

"Wane ya sani ko Shugaban yana fama da wata rashin lafiyan da tafi rashin iya magana? Wannan irin rufa-rufan wasa ne kawai irin na 'yan kwaikwayo.

"Abun takaici ne yadda wasu suka maida mulkin Najeriya kamar wasan yara."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel