Saraki ya aika sakon sallah ga 'yan Najeriya

Saraki ya aika sakon sallah ga 'yan Najeriya

- Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya aika da gaisuwar Salla ga ‘Yan Najeriya

- A cikin gaisuwar sa, ya bukaci ‘Yan Najeriya da su ci gaba da yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’an samun lafiya

Duk da cewan gwamnatin tarayya ta kuma jan sa zuwa kotu, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi ma shugaban kasa Buhari addu’a.

A cikin sakon gaisuwar Sallan sa Saraki ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi ma shugaban kasa addu’a, wanda ya koma birnin Landan don ci gaba da jinyatun ranar 7 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai kammala wa'adin mulkin sa - Osinbajo

Ga sakon Saraki kamar haka: “A yayinda muke bikin Sallah, Ina kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi ma shugaban kasar mu addu’an samun lafiya.”

Idan zaku tuna a baya NAIJ.com ta rahoto cewa a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni alkalin alkalai na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami , ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta daukaka karar hukuncin kotun da’ar maiakata a kan Bukola Saraki.

Malami ya ce jajircewarsa gurin yaki da rashawa ne ya sa ya yanke shawarar daukaka karar.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel