Shugaba Buhari zai kammala wa'adin mulkin sa - Osinbajo

Shugaba Buhari zai kammala wa'adin mulkin sa - Osinbajo

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kammala wa’adin mulkin sa cikin koshin lafiya

- Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan cike da karfin gwiwa

- Osinbajo ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya karbi tawagar musulman babban birnin tarayya a ranar Sallah

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kammala wa’adin mulkin sa har 2019 cikin koshin lafiya.

Ya fadi hakan ne a gidansa na Aguda dake fadar shugaban kasa, Abuja lokacin da ya tarbi tawagar musulman babban birnin tarayya, karkashin jagorancin minister Muhammad Bello wanda suka kai masa ziyarar Sallah.

KU KARANTA KUMA: Fani-Kayode ya soki shugaba Buhari kan sakon murya na sallah

Shugaba Buhari zai kammala wa'adin mulkin sa - Osinbajo

Osinbajo da Yusuf Buhari

A cewar sa: “Muna addu’a a kullun, kuma mun san cewa Allah madaukakin sarki, da muke bauta ma wa, zai dawo mana da shugaban kasar mu gida cikin koshin lafiya.

“Kuma zai bauta wa kasar nan da zuciya daya; kamar yadda yake bauta wa kasar tun daga lokacin da yake saurayi."

Shugaba Buhari zai kammala wa'adin mulkin sa - Osinbajo

Osinbajo da Malam Lawal Daura

Ya kuma ba tawagar tabbacin cewa gwamnati mai ci zata yi duk abun da ya dace don ganin dorewar zaman lafiya da hadin kan kasar.

NAIJ.com ta tattaro cewa wadanda suka halarci taron sun hada da sanata mai wakiltan babban birnin tarayya, Philip Aduda, mukaddashin shugaban masallacin tarayya, Mohammad Kabir Adamu, shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, sashin babban birnin tarayya, Reverend Samson Jonah da kuma dan shugaban kasa, Yusuf Buhari.

Sauran sun hada da shugaban alkalan Najeriya; Justis Walter Onnoghen, mukaddashin hukumar EFCC, Ibrahim Magu, mai ba kasa shawara a harkan tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), Darakta Janar na hukumar DSS, Malam Lawal Daura da sauran mambobin majalisar dokoki.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel