Fani-Kayode ya soki shugaba Buhari kan sakon murya na sallah

Fani-Kayode ya soki shugaba Buhari kan sakon murya na sallah

- Tsohon ministan dake kula da sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya kuma sukar fadar shugaban kasa

- Jigon na PDP ya yi zargin cewa ba shugaba Buhari bane ya yi jawabi ga kasar a sakon sallah da aka saki a jiya

- Ya soki sakon shugaban kasar wanda yay i jawabi ga kasar cikin harshen Hausa

Tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode ya yi zargin cewa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari bane ya yi magana a sakon murya da aka saki a jiya sallah.

Da farko NAIJ.com ta rahoto cewa fadar shugaban kasa ta saki sakon muryar shugaban kasa Buhari ga ‘yan Najeriya don kore rahotanni dake cewa yana fama da matsalar rashin magana.

Fani Kayode wani jigon jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a shafin tweeter ya ce: “Ba shugaban kasa Buhari bane ya yi magana a sakon murya na sallah da aka saki. Sannan kuma koma wanenene yay i jawabi ga kasar cikin harshen Hausa bai kyauta ba.”

A cewar wani rahoto da NAIJ.com ta kawo da farko, Buhari ya aika sakon gaisuwa ga musulman Najeriya a ranar bikin karamar sallah.

A cewar wata sanarwa daga kakakin shugaban kasar Garba Shehu, Buhari ya bukaci al’umman Najeriya da su zauna lafiya da kuma kore duk wani jawabi da zai ta da zaune tsaye.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel