Babu abin da ya hada mu da kasar Biyafara, mu yankin mu daban da nasu – Mutanen jihar Akwa-Ibom

Babu abin da ya hada mu da kasar Biyafara, mu yankin mu daban da nasu – Mutanen jihar Akwa-Ibom

- Wata kungiyar mutanen jihar Akwa-Ibom ta yi tur da kungiyar masu fafutukar neman Biyafara

- Ta ce babu abun da ya hada su da ita domin ba al'addun su daya ba

Wata kungiyar mutanen jihar Akwa-Ibom ta gargadi kungiyar masu fafutukar neman kasar Biyafara da su daina saka jihar Akwa-Ibom a cikin taswirar kasar Biyafara da suke nema.

Kungiyar ta ce babu abin da ya hada su da ‘yan kabilar Igbo.

KU KARANTA KUMA: Sakon Shugaba Buhari na bikin Idi ya kawo matsala

“Al’adar mu dabam, yarukan mu dabam, yadda muke komai na mu ba iri daya bane saboda haka suje can su ci gaba da neman kasar su ta Biyafara kawai idan har ta yiwu za mu taya su murna sannan mu yi musu ban kwana amma ba da mu ba.”

Kungiyar ta ce ita aladunta ya yi kama ne da na mutanen yankin Kudu Maso Kudu wanda inda take Kenan yanzu amma ba ‘yan Kabilar Igbo ba.

“Al’adun mu daya da mutanen yankinmu da ya hada da Jihohin Ribas, Cross-Ribas, Edo, Delta, da Bayelsa.”

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Nnmadi Kanu yayi wa Jama'ar sa jawabi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel