Sakon Shugaba Buhari na bikin Idi ya kawo matsala

Sakon Shugaba Buhari na bikin Idi ya kawo matsala

– Sakon da Shugaba Buhari ya aiko domin Sallah ya kawo rikici

– Wasu sun ce sam bai dace Shugaban kasa yayi magana da Hausa ba

– Tun lokacin da Shugaban ya bar Najeriya sai wannan karo a ka ji labarin sa

Jiya ne Shugaba Buhari ya aiko sakon Sallah ga ‘Yan Najeriya . An soki Shugaban bayan yayi magana da Musulmai da Hausa. Wasu dai na ganin hakan ma kara jagwalgwala lamarin yayi.

Sakon Shugaba Buhari na bikin Idi ya kawo matsala

Sakon Buhari na Sallah ya jawo rikici

A jiya ne ta bakin BBC Hausa mu ka ji Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sako ga mutanen Najeriya lokacin da ake shirin bikin karamar Sallah. Kafin nan ma akwai wadanda ke ganin Shugaban kasar yana cikin wani mawuyacin hali ko ma ya rasu.

KU KARANTA: Izala tayi kira ga Shugaba Buhari

Ganin akwai Musulmai a kasar da ba su jin Hausa, hakan ta sa ake ganin aika sakon da Hausa sam bai dace ba. Kun ji cewa masu nazari kuma sun tabbatar da cewa muryar shugaban ce ba kage ba amma dai wasu na da ja.

Shugaban kasar dai ya godewa ‘Yan Najeriya game da irin addu’o’in da aka rika masa yayin da yake fama da jinya. Wasu dai ba shakka muryar Shugaban kasar ya kwantar masu da hankali.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Nnmadi Kanu yayi wa Jama'ar sa jawabi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel