Sarkin musulmi ya yi magana mai karfi a kan gwamnatin Buhari a sakon sallah

Sarkin musulmi ya yi magana mai karfi a kan gwamnatin Buhari a sakon sallah

- Sarkin Sultan na Sokoto, Muhammad Sa'ad Abubakar ya kira gwamnatin tarayya da ta bincike yadda makiyaya ke samu makamai

- Sarkin Musulmi ya ce ainihin makiyaya ba sa yawo ko kuma kiwa da bindigogi

- Sultan ya shawarci gwamnatin tarayya cewa ta dauki matakin mai tsanani a kan makiyaya masu yawo da makamai don rage hare-hare

Sarkin Musulmi mai martaba Muhammad Sa'ad Abubakar, ya ce ainihin makiyaya suna kiwo daga shanu zai sandunansu kawai, ba sa yawo da bindigogi.

Sarkin Musulmi a cikin sakonsa na karamar sallah wato Eid-el Fitr ga ‘yan Najeriya ya kira gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasar, Muhammadu Buhari da babban murya da su bincike inda makiyaya nan masu yawo da bindigogi ke samu makamai wanda suke amfani da ita wajen kai hare hare ga al'ummomin kasar nan.

Ya ce: "Hakikanin Fulani makiyayan ba sa kiwo ko yawo da bindigogi; suna kiwo ne kawai tare da shanu da kuma sandunansu”.

Sarkin musulmi ya yi magana mai karfi a kan gwamnatin Buhari a sakon sallah

Sarkin Musulmi mai martaba Muhammad Sa'ad Abubakar

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Sultan ya ci gaba da cewa: “Babu shaka akwai bata gari a tsakanin Fulani makiyayan, amma wadanda ke dauke da makamai da kuma kashe-kashen ba makiyaya ne”.

“Wadanda ke dauke da makamai miyagu ne a tsakanin makiyayan, kuma ya kamata gwamnati ta dauki mataki a kan su”.

KU KARANTA: Sallah: Uwargidan Buhari, Aisha ta bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa mijinta addu’a

Ya kamata gwamnati ta kafa kwamitin bincike don gano inda wadannan makiyaya ke samun makamai kuma ta dauki mataki mai tsanani don rage wadannan hare-haren.

Sarkin Musulmi ya yaba wa gwamnatin tyarayya a matakan magance hare haren ta’addanci a arewa maso gabashin kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku saurari tsohon direban Bishof David Abioye na Living Faith Church wanda ya karbi addinin musulunci bayan ficewa daga cocin

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel