Sallah: Uwargidan Buhari, Aisha ta bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa mijinta addu’a

Sallah: Uwargidan Buhari, Aisha ta bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa mijinta addu’a

- Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha ta gode ma ‘yan Najeriya kan irin gudunmuwar da suke ba mijinta

- Ta bayyana dalilin da zai sa ‘yan Najeriya su ci gaba da yi mai addu’a

- Ta kara da cewa ‘yan Najeriya su kara kaimi gurin addu’a

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta bukaci ‘yan Najeriya da suka kara kaimi gurin addu’a don warzuwan zaman lafiya da ci gaban kasar.

Punch ta rahoto cewa uwargidan Buhari ta fadi hakan ne a sakon fatan alkhairi da babban hadimar shugaban kasa, Dr Hajo Sani ta karanta a ranar Lahadi, 25 ga watan Yuni a Abuja.

NAIJ.com ta tattaro cewa uwargidan Buhari ta kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi ma shugaban kasa addu’an samun lafiya.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 4 da Shugaba Buhari ya fada a sakon Sallar Idi

Sallah: Uwargidan Buhari, Aisha ta bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa mijinta addu’a

Sallah: Uwargidan Buhari, Aisha ta bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa mijinta addu’a

A cewar uwargidan shugaban kasar. “bikin sallah nuni ne ga cewan water Ramadan ya kare.

"Ina umartan ‘yan Najeriya da Musulmai kan suyi amfani da wannan dama su nemi kusanci ga Allah,” cewar ta.

Uwargidan shugaban kasa ta yi sallar idi a masallacin barikin Mambila wanda limamin masallacin, Manjo Hamisu Mustapha ya jagoranta a Abuja.

Aisha ta samu rakiyan Sani, ahlin gidan ta da wasu makusantan ta.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa ministan wasanni Solomon Dalung ya ce Buhari zai dawo nan bada jimawa ba.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel