Wani na hannun daman Buhari ya yi babban magana kan shugaban kasa; ku karanta

Wani na hannun daman Buhari ya yi babban magana kan shugaban kasa; ku karanta

- Wani jigon dan siyasa ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ya yi murabus idan ya san ba zai iya ci gaba da jagorancin kasar ba

- Tsohon babban Hafsan Sojojin Najeriya ya ce yin murabus zai fi wa shugaban kasar alheri kafin a bata masa suna

- Fadar shugaban kasa ta saki sakon muryar Shugaba Buhari don yi watsi da rahotanni dake cewa shugaban na fama da matsalar rashin magana

Tsohon babban Hafsan Sojojin Najeriya, kuma shahararren memba na wata tsohuwar jam'iyyar da aka sani da National Democratic Coalition, Janar Alani Akinrinade, ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ya yi murabus idan ba zai iya ci gaba da shugabancin kasar ba.

A wata hira da jaridar Punch, Janar Akinrinade ya ce, yin marabus shi ne mafi alheri ga shugaban kasar kafin sunan sa ya baci a kan son mulki.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Janar Akinrinade ya nuna cewa Najeriya zata ci gaba da kasancewa, babu abin da zai same ta idan shugaban ya yi murabus

Wani na hannun daman Buhari ya yi babban magana kan shugabajn kasa; ku karanta

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu jami'an gwamnati a fadar shugaban kasa kafin tafiyarsa zuwa Landan

Akinrinade ya ce: “Na tabbata shugaban kasa da wadanda ke kewaye da shi sun san cewa wannan magana ba wai batun son ra’ayi na bane. Idan shugaban kasar ba shi da isashen lafiya na jagorancin kasar mafi alheri shine ya yi murabus kafin a bata masa suna”.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta saki muyar Buhari a lokacin da yake aike ma ‘yan Najeriya sakon sallah

NAIJ.com ta ruwaito a baya bayan nan cewa fadar shugaban kasa ta saki sakon muryar shugaban kasa Muhammadu Buhari ga ‘yan Najeriya domin yin watsi da rahotanni dake cewa shugaban kasar na fama da matsalar rashin magana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan komawar shugaba Buhari Landan don duba lafiyarsa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel