Fadar shugaban kasa ta saki muyar Buhari a lokacin da yake aike ma ‘yan Najeriya sakon sallah

Fadar shugaban kasa ta saki muyar Buhari a lokacin da yake aike ma ‘yan Najeriya sakon sallah

- Fadar shugaban kasa ta saki sakon muryar shugaban kasa Buhari a shafin BBC da sauran tashoshin radiyo

- Dukkan wannan a kokarin karyata jita-jitan cewa shugaban kasa na fama da matsalar magana

Fadar shugaban kasa ta saki sakon muryar shugaban kasa Muhammadu Buhari ga ‘yan Najeriya domin yin watsi da rahotanni dake cewa shugaban kasar na fama da matsalar rashin magana.

A yan kwanakin nan an samu rahotanni a shafukan zumunta dake ikirarin cewa shugaban kasar na fama da matsalar rashin magana da cutar mantuwa.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 4 da Shugaba Buhari ya fada a sakon Sallar Idi

‘Yan Najeriya da dama sun bukaci shugaban kasar da ya yi magana ga ‘yan Najeriya domin su tabbatar da cewa yana cikin hali mai kyau.

Buhari ya gode masu bisa tarin addu’o’insu a gare shi.

Shugaban kasa Buhari ya bar kasar a ranar 7 ga watan Mayu zuwa birnin Landan don ci gaba da jinya.

A halin da ake ciki, ministan wasanni, Solomon Dalung ya ce shugaban kasar na nan dawowa nan ba da jimawa ba.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel