Hudubar Idi: Ka ji kiran da wani Limami yayi kira ga ‘Yan Najeriya

Hudubar Idi: Ka ji kiran da wani Limami yayi kira ga ‘Yan Najeriya

– Babban Limamin masallacin Jami’ar A.B.U yayi kira ga ‘Yan kasa

– Sheikh Salihu Abubakar ya nemi ‘Yan Najeriya su daina dogaro da Gwamnati

– Malamin yayi wa Kasar Najeriya da sauran Jama’a addu’a

Sheikh Salihu Abubakar ya kira Jama’a su tashi tsaye. A cewar babban Shehin ba dole Gwamnati ce za tayi gyara ba. Malamin yayi wa kasa da Shugaba Buhari addu’a.

Hudubar Idi: Ka ji kiran da wani Limami yayi kira ga ‘Yan Najeriya

Wasu Musulman Najeriya a filin Idi

Babban Limamin masallacin Jami’ar A.B.U watau Ahmadu Bello Sheikh Salihu Santalma Abubakar yayi kira ga ‘Yan Najeriya da su tashi tsaye kuma su daina dogara ko-ca-kam kan Gwamnatin Kasar. Haka kuma Malamin yayi wa Shugaban kasa da Jama’a duk addua.

KU KARANTA: Sakon Shugaba Buhari na karamar sallah

Hudubar Idi: Ka ji kiran da wani Limami yayi kira ga ‘Yan Najeriya

Babban Limamin masallacin Jami’ar A.B.U a karshe daga hagu

Shehin Malamin yayi kira da ‘Yan kasa su dage a duk matakin da su ke na kawo gyara. Sheikh S.S Abubakar ya nemi Jama’a da su kawo gyara domin za a tambaye su duk inda su ka samu kan su domin kawo gyara na gari a cikin al’umma.

Kun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiko sakon Sallah ga ‘Yan Najeriya ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu. Shugaban Kasar yayi godiya inda ya kuma nemi a zauna lafiya a Najeriya.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jagoran Biyafara yayi wa Jama'ar Ibo bayani a Jihar Abiya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel