Rundunar ‘yan sanda ta ce tana samun matsa lamba kan ta saki Evans

Rundunar ‘yan sanda ta ce tana samun matsa lamba kan ta saki Evans

- Mukaddashin kwamishinan jihar Lagas Galadanshi Dasuki ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Asabar, 24 ga watan Yuni

- Dasuki y ace ‘yan sanda basa gaggawa don sakin mai garkuwa da mutanen

- Ya ce hukumar na son ta gama tambayan Evans sannan kuma tayi amfani da bayanan da ta samu daga gare shi gurin kama sauran masu garkuwa da mutane

Rundunar ‘yan sandan jihar Lagas ta nemi dauki kan cewa ana hura mata wutan ta saki gawurtaccen biloniya mai garkuwa da mutane Chukwudumeme Onwuamadike alias Evans.

Daily Trust ta rahoto cewa Mukaddashin kwamishinan jihar Lagas Galadanshi Dasuki ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Asabar, 24 ga watan Yuni a hedkwatan su dake Ikeja cewa ‘yan sanda basa gaggawa don sakin Evans duk da kiraye-kiraye da suke samu daga hedkwata daban-daban kan suyi hakan.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: ‘Yan sanda sun kama Sojan da ke taimakawa mai garkuwa da mutane, Evans

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa rundunar ‘yan sanda sun kama wani soja a hukumar sojin Najeriya, Victor Chukwunonso, sakamakon samun shi da akayi da hannu dumu-dumu gurin taimaka wa babban mai garkuwa da mutanen nan, Chukwudimeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans.

Chukunonso dauke da lambar soji NO: 09/NA/64/6317 na daga cikin masu jami’an dake yi ma hukumar soji kida, a barikin Abatti, Surulere, Lagas.

Rahotanni sun kawo cewa jami’an sashin masu hikima na sufeto janar na ‘yan sanda ne suka kama shi a ranar Lahadi.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel