Abubuwa 4 da Shugaba Buhari ya fada a sakon Sallar Idi

Abubuwa 4 da Shugaba Buhari ya fada a sakon Sallar Idi

– Shugaban Buhari ya aika sakon sallah ga mutanen Najeriya

– Shugaban ya taya daukacin ‘Yan kasar murnar wannan rana

– Ana ma kuma sa ran Shugaban kasar ya dawo kwanan nan

Shugaba Buhari ya aiko sakon Sallah ga ‘Yan Najeriya jiya. Shugaban Kasar da je jinya yayi kira a zauna lafiya. Haka kuma Shugaban ya nuna godiya da addu’o’in da ake yi masa

Jama’a sun ji dadin jin muryar Shugaban kasa Buhari

Abubuwa 4 da Shugaba Buhari ya fada a sakon Sallar Idi

KU KARANTA: Bikin Sallah: Sakon Shugaban kasa Buhari

1. Addu’o’i

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna godiya da addu’o’in da mutanen Najeriya ke yi masa domin samun lafiya ya kuma cika alkawura a sakon goron sallar sa.

2. Murnar Sallah

Shugaban ya taya daukacin ‘yan kasar murnar kammala azumi da kuma shirin karamar Sallah a yau.

KU KARANTA: Jama'a sun ji dadi bayan jin kalaman Buhari

3. Zama lafiya

Shugaba Muhammadu Buhari yayi kira ayi watsi da maganganun da za su raba kan Jama’a a zauna lafiya a Najeriya.

4. Damina

Kamar ko yaushe Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya roki Ubangiji ya ba mu damina mai albarka a Najeriya.

Kamar yadda ku ka ji masu nazari kuma sun tabbatar da cewa muryar shugaban ce ba kage ba, wanda wannan ya sa hankalin da dama na kasar ya kwanta.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kullum abu daya a Najeriya wajen harkar kasafin kudin kasa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel