Sallar Idi: Sakon Shugaba Buhari ya kwantar da hankalin ‘Yan Najeriya

Sallar Idi: Sakon Shugaba Buhari ya kwantar da hankalin ‘Yan Najeriya

– Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sako ga mutanen Najeriya

– Ana ma dai sa ran Shugaban kasar ya kusa dawowa Najeriya

– Mun ji kishin-kishin din cewa dimuwa ta fara kama Shugaban kasar

Shugaba Buhari ya aiko sakon Sallah ga ‘Yan Najeriya ta bakin Garba Shehu. Shugaban Kasar yayi godiya inda ya nemi a zauna lafiya a Najeriya. Masu nazari kuma sun tabbatar da cewa muryar shugaban ce ba kage ba. Wannan ya sa hankalin da dama na kasar ya kwanta.

Sallar Idi: Sakon Shugaba Buhari ya kwantar da hankalin ‘Yan Najeriya

Shugaban Kasa Buhari yayi godiya ga 'Yan Najeriya

Yayin da wasu ke maganar cewa rashin lafiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na kara tabarbarewa sai ga shi ya aiko sakon Sallah ga ‘Yan Najeriya inda yayi kira a cigaba da zama lafiya a kasa tare da addu’a domin sauke nauyin da ke kan Shugabannin.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya ja junnen 'Yan kasa

Sallar Idi: Sakon Shugaba Buhari ya kwantar da hankalin ‘Yan Najeriya

Ana sa rai Shugaban kasa Buhari ya kusa dawowa Najeriya

Shugaban kasar dai ya godewa ‘Yan Najeriya game da irin addu’o’in da aka rika masa yayin da yake fama da jinya. Masu nazari dai sun ce ba shakka cewa muryar Shugaban kasar ce don kuwa ya taba abubuwan da su ke faruwa a kasa.

Makon can ne Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Kwankwaso yace Allah ne zai yi zabi a zabe mai zuwa na 2019. Kwankwaso yace kasancewar Shugaba Buhari na asibiti ba ya nufin sauran ‘Yan siyasar sun fi shi lafiya ko kuma ba zai tsaya takara ba don abu ne na Allah.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana dandazo domin ganawa da Nnamdi Kanu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel