Shugaba Buhari zai dawo Najeriya cikin sabon mako – mataimakan sa

Shugaba Buhari zai dawo Najeriya cikin sabon mako – mataimakan sa

- An rahoto cewa shugaban kasa Buhari ya ji sauki sosai sakamakon kulawar da likitansa ya basa kuma yana iya dawowa nan da ‘yan kwanaki

- Wani mataimakin sa ya yi ikirarin cewa an sa wa shugaban kasar jini don ya taimaka masa gurin samun lafiya

- Wata majiya ta ce rashin maganar Buhari na dan wani lokaci kalilan ne

Sahara Reporters sun rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin dawowa gida Najeriya nan da yan wasu kwananki bayan ya yi kimanin watanni biyu a kasar waje.

A cewar rahoton, hadiman shugaban kasa biyu sun bayyana lokacin da shugaban kasar zai dawo a ranar Juma’a, 23 ga watan Yuni.

A cewar su, shugaban kasar ya ji sauki sosai.

NAIJ.com ta rahoto da farko cewa ministan wasanni Solomon Dalung ya sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo kasar nan ba da jimawa ba.

Dalung ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuni a shafin Facebook. Ministan bai fadi ainahin ranar da shugaban kasar zai dawo ba.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel