Masu garkuwa da mutane 2, 000 ke garkame yanzu – IGP, Ibrahim Idris

Masu garkuwa da mutane 2, 000 ke garkame yanzu – IGP, Ibrahim Idris

Sifeto Janar na hukumar yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, yace akalla masu garkuwa da mutane 200 ne hukumar ta kama a fadin tarayya.

Sifeto janar din yayi wannan bayani ne a wata hira da kungiyoyin fafutuka tare da shugaban hukumar INEC a Abuja jiya Juma’ a, yace hukumar yan sandan suna kama daruruwan masu garkuwa da mutane kulli yaumin. ya bayar da shawaran cewa a tsananta ukubar duk wanda aka kama Kaman yadda akayi a jihar Anambra da Legas da kuma samar da kotu na musamman domin gurfanar a su.

Yace babban mai garkuwa da mutane ya umurci yaransa kada su sayi dukiya a Najeriya ko kuma gina gidaje a jihar Anambra saboda idan aka kamasu za’a rusa gidajen, saboda haka ya gina gidajensa a Legas da kasar Ghana.

Masu garkuwa da mutane 2, 000 ke garkame yanzu – IGP, Ibrahim Idris

Masu garkuwa da mutane 2, 000 ke garkame yanzu – IGP, Ibrahim Idris

Yace kasar nan a yanzu babu isassun jami’an yan sanda. Yace hukumar yansanda jami’ai 10,000 kacal ta dauka shekaran da ya gabata. Yace adadin yansandan da ake bukata a Najeriya 700,000 ne amma 308,000 kawai ake da shi.

KU KARANTA: Saudiya da wasu kasashe sun ga wata

Yace domin cimma lamban majalisar dinkin duniya, ya kamata a dauki jami’ai 30,000 kowani shekara na tsawon shekaru 5 masu zuwa.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel