Duk wanda yayi kokarin kama matasan Arewa rikici zai jawo – Junaid Mohammed

Duk wanda yayi kokarin kama matasan Arewa rikici zai jawo – Junaid Mohammed

– Junaid Mohammed yace kama matasan Arewa akan maganar wa’adin Igbo zai jawo rikici a Arewa

- Mohammed ya tuhumci gwamnatin tarayya da son kai wajen mayar da hankali wajen yan Arewa sabanin na yan kudu

Maganar damke matasan da suka baiwa yan kabilar Igbo wa’adi ya bar baya da kura yayinda wasu dattijan Arewa sukace sam babu wanda ya isa ya damke wani matashi.

Wani tsohon dan majalisa, Dakta Junaid Mohammed yace damke wadannan matasan ba karamin rikici ya janyo a arewa ba.

Junaid ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a yayinda yake hira da jaridar Vanguard.

Yace gwamnatin tarayya da nuna rashin hankali wajen nuna son kai tsakanin matasan yankin Arewa da na kudacin Najeriya.

Duk wanda yayi kokarin kama matasan Arewa rikici zai jawo – Junaid Mohammed

Duk wanda yayi kokarin kama matasan Arewa rikici zai jawo – Junaid Mohammed

Yace: “ Barazanar damke matasa a fahimta ta zai bar baya da kura kuma bai dace ba. Dalili shine yadda abubuwa suka a Najeriya yazu, kowani da kasa na da hakkin kasuwanci a kowani sashen kasar.

KU KARANTA: Saudiyya da wasu kasashe 15 sun ga wata

“Amma gwamnatin tayi ko oho ta bari kungiyar IPOB wanda manyan yan siyasan Igbo ke daukan nauyi su dinga sakin jawabai yadda suka ga dama.”

“Saboda haka, duk wani kokarin damke matasan Arewa rikici zai sabbasa. Ni mazaunin Kano ne kuma da gwamnatin jihar Kaduna ta damke wani matashi kwanakin baya, da an ga tashin hankali.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel