A yanke ma Evans hukuncin kisa kawai – Sifeton yan sanda

A yanke ma Evans hukuncin kisa kawai – Sifeton yan sanda

Sifeto Janar na hukumar yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya bayar da shawaran cewa a yankewa masu garkuwa da mutanen da aka kama hukuncin kisa kawai.

Sifeto janar din yayi wannan bayani ne a wata hira da kungiyoyin fafutuka a Abuja jiya Juma’ a, yace ayi amfani da babban mai garkuwa da mutane Chukwudidumeme Onuamadike, a.k.a Evans, a matsayin izina ga sauran.

Idris yace “ Evans ya canza fuskar garkuwa da mutane a wannan kasan” yace a samu cewa ya karbi fansan $1million sau 6 kadai ya isa matasa su fara wannan sana’ar sharrin.

Babban hafsan yan sandan yace ya kamata a sake duba dokokin ukubantar da masu garkuwa da mutane kuma a tsananta su.

Kasugumin mai garkuwa da mutane ‘Evans’: A yanke masa hukuncin kisa kawai – Sifeton yan sanda

Kasugumin mai garkuwa da mutane ‘Evans’: A yanke masa hukuncin kisa kawai – Sifeton yan sanda

Ya kamata mu fara tunanin ukuba tsattsaura da kuma yiwuwan bude kotuna na musamman domin kula da harkokin garkuwa da kai.

“Kulli yaumin muna damke daruruwan masu garkuwa da mutane. Muyi tunanin yadda zamu duba dokokinmu da kuma sanya takunkunmi kamar yadda ake da shi a jihohi irinsu Anambra, Lagos, Kano da Imo.

KU KARANTA: PDP ta jinjinawa Yemi Osinbajo

“Wasu yan kauye basu fahimta, kawai suna ganin ana nuna mutane da Talabijin kuma ta kare a anan.

“Kamar yadda bayyana garkuwa da mutane ya zama babban kalubale garemu a wannan kasa. Amma, ina farin cikin cewa kudan kasha 80 cikin 100 karan da aka kawo ma yansanda, mun damke su.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel