YANZU-YANZU: Boko Haram ta saki bidiyon nuna cewa tayi garkuwa da jami’an yan sanda

YANZU-YANZU: Boko Haram ta saki bidiyon nuna cewa tayi garkuwa da jami’an yan sanda

- Kwamishanan yan sandan jihar, Chukwu yace babu dan sandan da ak kashe ko aka sace

- Rahoto ya bayyana cewa Boko Haram tayi garkuwa da akalla jami’an yan sanda 16

Jaridar Sahara Reporters tana bada rahoton cewa yan kungiyar Boko Haram ta saki wani bidiyo da ke nuna cewa sunyi garkuwa da wasu jami’an hukumar yan sanda kwanakin baya.

Jaridar ta saki hoton ne a shafin ra’ayi da sada zumuntarta na Tuwita a yau Asabar, 24 ga watan Yuni.

Zaku tuna cewa NAIJ.com ta bada rahoton cewa hukumar yan sandan jihar Borno ta tabbatar da cewa lallai an hallaka jami’an yan sanda 2 a wata harin da Boko Haram ta kai musu a hanyar Maiduguri- Damboa.

KU KARANTA: Hukumar yansanda zata dau wani sabon mataki

Kwamishanan yan sandan jihar Damian Chukwu, ya tabbatar a ranan 20 ga watan Yuni cewa wadanda suka hallaka ya kunshi jami’in dan sanda daya da direban mota.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel