Zamu janye dukkan yan sandan da ke tsare masu hannu da shuni – IGP Ibrahim Idris

Zamu janye dukkan yan sandan da ke tsare masu hannu da shuni – IGP Ibrahim Idris

Sifeto Janar na yansanda, Ibrahim Idris, yace hukumar yan sandan ta shirya janye dukkan yan sandan da ke like da masu kudi a kasan nan zuwa bariki.

Game da cewarsa, za’ayi hakan ne domin kusanta yan sanda da yan Najeriya.

Idris ya bayyana wannan ne ranan Juma’a a waya hira da kungiyoyin fafutuka a birnin tarayya, Abuja.

Yace: “ Zamu janye dukkan jami’an yan sanda zuwa bariki domin mayar da hankulansu wajen fuskantar karya dokoki.

“Wannan yana nufin cewa zamu daina tura jami’an yan sanda tsare masu kudin kasa saboda ba wajen aikinsu kenan ba.”

“Zamuyi wannan ne domin samun isassun jami’an musamman wajen dakile harkokin garkuwa da mutane.”

Zamu janye dukkan yan sandan da ke tsare masu hannu da shuni – IGP Ibrahim Idris

Zamu janye dukkan yan sandan da ke tsare masu hannu da shuni – IGP Ibrahim Idris

Idris yace an yanke wannan shawara ne musamman domin dakile garkuwa da mutane da ya zama ruwan dare kuma ya zama kalubale da hukuma saboda tana samu kuka kulli yaumin.

KU KARANTA: Kowa yabi: PDP ta jinjinawa Osinbajo

Ya bada shawaran kafa kotuna na musamman domin hukuncin harkokin garkuwa da mutane.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel