Kin biyan haraji: Abu 1 tilo da zai hana Messi zuwa gidan yari

- Akwai yiwuwar shahararren dan wasan Barcelona Lionel Messi zai kaucewa daurin wata 21 a gidan yari inda ya zabi ya biya tara, kamar yadda rahotanni daga kasar Spain suka bayyana.

- Wata kotu ce a Spain ta samu dan wasan da laifin zambar haraji.

Babban mai gabatar da karar kasar zai musanyawa Messi zaman gidan yari zuwa biyan tarar euro 255,000 wato zai biya euro 400 a kowace rana idan da zaman gidan kason zai yi.

Kotunan Spain ne suke da ikon yanke hukuncin karshe game da batun.

NAIJ.com ta samu labarin cewa an samu Messi da mahaifinsa Jorge da laifin zambar haraji a Spain fiye da euro miliyan hudu tsakanin shekarar 2007 zuwa 2009.

An ci dan wasan tarar euro miliyan biyu, mahaifinsu kuma euro miliyan daya da rabi.

A watan jiya ne kotun koli ta yi watsi da daukaka karar da Messi ya yi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

NAIJ.com
Mailfire view pixel