Yunkurin raba kasa: Jam'iyyar adawa ta PDP ta jinjinawa Osinbajo

Yunkurin raba kasa: Jam'iyyar adawa ta PDP ta jinjinawa Osinbajo

Jam’iyyar PDP bangaren sanata Makarfi ta jinjina wa mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, dangane da irin matakan da ya ke dauka domin shawo kan matasalar miyagun kalaman da wasu sassan Nijeriya ke jefa wa junan su.

Shugaban riko na jam’iyyar PDP Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya bayyana haka, a wani taron ganawa da manema labarai da ya gudana a Abuja, inda ya ce Farfesa Yemi Osinbajo ya cancanci a yaba da kwazon sa.

Yunkurin raba kasa: Jam'iyyar adawa ta PDP ta jinjinawa Osinbajo

Yunkurin raba kasa: Jam'iyyar adawa ta PDP ta jinjinawa Osinbajo

NAIJ.com ta samu labarin cewa Sanatan, ya kuma ja hankalin gwamnatin tarayya da cewa, ta tabbatar da ganin duk matakan da za ta dauka wani bangare na kasar nan ba zai yi korafin an maida shi saniyar ware ba.

Makarfi ya kuma bukaci shugabannin al’umma na kowane mataki, su lalubo hanyoyin da su ka dace wajen magance kalubalen da Nijeriya ke fuskanta.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel