Kasa-daya-al'umma daya: Wani Inyamuri a Kano ya dinkawa Almajirai 30 kayan Sallah

Kasa-daya-al'umma daya: Wani Inyamuri a Kano ya dinkawa Almajirai 30 kayan Sallah

Hausawa suka ce “Ba duka aka taru aka zama daya ba,” tabbas malam Bahaushe yayi gaskiya a wannan magana tashi, yayin da wasu yan kabilar Igbo karkashin jagorancin Nmandi Kanu, suka dukufa wajen ganin cewa kasarnan ta wargaje.

A gefe guda kuma wasu yan kabilar Igbo sun dukufa wajen ganin dorewar kasarnan kasa guda.

Ba komai ne yasa nace haka ba sai ganin yadda rahotanni ke cewa wani dan kabilar Igbo dake zaune a kasuwar Sabon Gari dake Kano ya tara Almajirai har guda 30 domin yi musu dinkin sallah.

Kasa-daya-al'umma daya: Wani Inyamuri a Kano ya dinkawa Almajirai 30 kayan Sallah

Kasa-daya-al'umma daya: Wani Inyamuri a Kano ya dinkawa Almajirai 30 kayan Sallah

NAIJ.com ta samu labarin cewa jama’a da dama a shafukan sada zumunta sun yaba da irin wannan kokari da mutumin yayi inda suka ce hakan zai kawo hadin kan kasa, musamman a wannan lokacin da ake musayar zafafan kalamai tsakanin kungiyoyi da suka fito daga yankin kudu maso gabas da kuma wadanda suka fito daga yankin Arewa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel