Biyafara: Maganganun Kwankwaso sun jefa sa cikin matsala

Biyafara: Maganganun Kwankwaso sun jefa sa cikin matsala

- Kungiyar Inyamurai sun soki kalaman Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

- Sun ce akwai kulalliya a cikin maganganun sa

- Kwankwaso dai yace bai dace a kama matasan nan da su kayi kira a kora 'yan Kabilar Igbo daga Arewa ba

Kungiyar Ohanaze ta soki kalaman tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Kwankwaso inda tace akwai kulalliya a cikin maganganun na sa.

Kwankwaso dai yace bai dace a kama matasan nan da su kayi kira a kora 'yan Kabilar Igbo daga Arewa ba.

Kalaman Kwankwaso kan Inyamurai sun tada kura.

KU KARANTA KUMA: An dakile shirin kai hare haren ta'addanci a ranar Sallah

Biyafara: Maganganun Kwankwaso sun jefa sa cikin matsala

Kungiya Inyamurai sun soki kalaman Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Ohanaze ta bakin Chuks Ibegbu tace babu fa wanda ya fi karfin dokar kasa don haka ma wannan maganar ba ta taso ba inda ta gargadi masu kokarin tada hankalin.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa tsohon Gwamnan Kaduna Balarabe Musa ya soki kalaman Sanatan.

Sanata Kwankwaso ya ba Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai shawarar matakin da ya kamata ya bi wajen kawo karshen rikicin da ke nema ya barke tsakanin Inyamurai da ‘Yan Arewa,yace tattaunawa ce hanyar zaman lafiya.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel